Jump to content

Harold Robbins

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Harold Robbins
Rayuwa
Haihuwa New York, 21 Mayu 1916
ƙasa Tarayyar Amurka
Mutuwa Palm Springs (mul) Fassara, 14 Oktoba 1997
Makwanci Forest Lawn Cemetery (en) Fassara
Yanayin mutuwa  (Gazawar zuciya)
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a marubuci, Marubuci da marubin wasannin kwaykwayo
Kyaututtuka
IMDb nm0730356
Harold Robbins

Harold Robbins (an haifeshi ranar 21 ga watan Mayu, 1916 - 14 ga watan Oktobar shekarar, 1997) marubucin Ba'amurke ne na shahararrun litattafai. Daya daga cikin marubutan da suka fi siyarwa na kowane lokaci[1], ya rubuta sama da littatfai 25 mafi kyawun siyarwa, sannan ya sayar da kwafi sama da miliyan 750 a cikin harsuna 32.

Farkon rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Robbins Harold Rubin a Birnin New York a cikin shekarar 1916, ɗane Frances "Fannie" Smith da Charles Rubin. Iyayensa sun kasance masu hijira Yahudawa masu ilimi daga Daular Rasha, mahaifinsa daga Odessa da mahaifiyarsa daga Neshwies (Nyasvizh), kudancin Minsk. Robbins daga baya sun yi iƙirarin ƙarya cewa shi maraya Bayahude ne wanda ya girma a gidan mazan Katolika.[2][3] Maimakon mahaifinsa, masanin harhada magunguna, da mahaifiyarsa, Blanche, suka rene shi a Brooklyn.

Harold Robbins

Robbins ya bar makarantar sakandare a ƙarshen 1920s don yin aiki a ayyuka daban-daban, ciki har da ɗan wasa, ɗan tseren littattafai, da magatakardar kaya a cikin masu siyar da kayan abinci. Hotunan Universal Pictures ne suka ɗauke shi aiki daga shekarar 1940 zuwa shekarar 1957, ya fara aiki a matsayin magatakarda kuma ya kai matsayin zartarwa.[4]