Albidaya wan Nihaya
Albidaya wan Nihaya | |
---|---|
Asali | |
Mawallafi | Ibn Kathir |
Online Computer Library Center | 32244065 |
Characteristics | |
Harshe | Larabci |
Albidaya wan Nihaya ((ألبدية والنهة "Farkon da karshen" ko kuma "Tarikh ibn kathir" yana daya daga cikin litafai da babban malamin sunnah Sheikh ibn Kathir ya rubuta a lokacin rayuwarsa, littafin dai na kunshe ne da tarihi tun farkon halittar duniyar ta yadda yazo a Qur'ani da Sunnar manzon Allah (amincin Allah ya tabbata a gareshi), tun daga halittar annabi Adam, da sauran annabawa har zuwa karni na takwas, zuwa haihuwar Annabi Muhammad (SAW), da sahabbansa da wa 'yanda suka biyo su na abubuwan da ya auku a zamaninsu wanda ya kamata mu sani dangane da su ,kuma littafin bai tsaya a kan tarihin abinda ya gabata ba kawai har da na abinda zai auku nan gaba, kamar su alamomin tashin kiyama: irinsu bayanar dujal, zuwan annabi Isah (AS) kamar yadda yazo a Qur'ani da Hadisi. Da kuma abubuwan da za su wakana a gobe kiyama na daga hisabi da yadda muminai zasu shiga aljannah, da kuma yadda 'yan wuta zasu shiga wuta.